in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta samu raguwar cutar shan-inna da kashi 50 cikin dari daga watan Afrilu zuwa Yuni na wannan shekara
2013-06-20 16:05:35 cri
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, da asusun taimakon yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun ce Najeriya ta samu raguwar cutar polio wato shan-inna da kashi 50 cikin dari daga watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar da muke ciki.

Najeriya tare da Pakistan da kuma Afghanistan sune kasashe uku kawai da suka rage a duniya, wadanda ke samun masu dauke da cutar shan-inna.

Geoffery Njoku, wani jami'in UNICEF wanda ya bayar da wata sanarwa a ranar Laraba a birnin Abuja cewa, Najeriya na samun ci gaba sosai ta fannin yaki da cutar shan-inna Kuma ya zuwa yanzu a cikin wannan shekara, an samun mutane 25 wadanda suke dauke da cutar a cikin jihohi 9, wanda ya ragu sosai idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara, wato mutane 54 a cikin jihohi 10.

Sanarwar ta ce, fiye da kashi 60 cikin dari na mutanen da suke dauke da cutar shan-inna a shekara ta 2013 a Najeriya, sun fito ne daga wuraren da ake samun matsalar tsaro, ciki har da Borno da Yobe, inda ake fuskantar wahalar yiwa yara allurar rigakafin cutar.

Bisa labarin da muka samu, an ce, yawan kananan yara da ba su karbi allurar rigakafin cutar shan-inna ba ya ragu sosai a cikin 'yan watannin nan a Najeriya, dalilin kuwa shi ne jama'a na kara samun ilmi da maida hankali a wannan fanni.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar WHO da asusun UNICEF za su ci gaba da marawa gwamnatin Najeriya baya, a kokarin taimakawa mata da yara a fannin yaki da cutar polio wato shan-inna.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China