in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron raya nahiyar Afrika a kasar Japan
2013-06-03 15:48:24 cri

A yau Litinin 3 ga wata, aka rufe taron raya nahiyar Afrika a kasar Japan bayan an zartas da yarjejeniyar Yokohama, wato sunan birnin da aka yi wannan taro, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashen Afrika 51.

Wannan yarjejeniyar ta bukaci a shimfida zaman lafiya da karko a nahiyar Afrika, domin samar da yanayi mai kyau ga bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar, sa'an nan a gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar ta hanyar kyautata manyan ababen more rayuwa ta karfin jama'a. Ban da haka, taron ya gabatar da wani shiri, wanda ya gabatar da manufofi, ayyuka da muradun da za a yi ciki hadda habaka sha'anin noma. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China