in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitocin Najeriya za su fara wani yajin aikin gama gari na kwanaki uku
2013-06-25 16:14:30 cri
Kungiyar likitocin Najeriya (NARD) ta kira mambobinta, a dukkan fadin kasa da su amsa kiranta na shiga yayin aikin kashedi na kwanaki uku da zai fara tun daga bakin ranar Laraba. Kungiyar NARD ta bayyana cewa, yajin aikin na da manufar yin Allah wadai da rashin kudaden da ake kebewa domin horar da likitocin kasa daga wajen gwamnatin tarayya. Kashedin kwanaki 21 da NARD ta aika wa gwamnati ya kare tun ranar 18 ga watan Yunin da muke ciki.

A yayin wani taron manema labarai da aka shirya yau da sati biyu da suka gabata a jami'ar Olabisi Onabanjo ta jihar Ogun dake kudu maso yammacin kasar, shugaban kungiyar Ismail Akinlade Lawal, ya yi gargadin cewa, akwai yiyuwar likitocin kasar baki daya su shiga yajin aiki bayan wannan kashedi na kwanaki 21.

Mista Lawal dake bayyana matsalar rashin kudaden da ake kebewa horar da likitocin kasa a cikin kasafin kudi na shekarar 2013, ya kara bayyana cewa, kungiyarsa ta baiwa gwamnatin tarayya lokaci da ta bullo da hanyoyin warware wannan matsala. Amma cikin wata sanarwar da ta biyo bayan taron kungiyar a ranar Litinin a Abeokuta, hedkwatar jihar Ogun, shugaban kungiyar NARD ya kira mambobin kungiyarsa da su shiga yajin aikin kashedi na gama gari domin yi Allah wadai da wannan shiru na gwamnatin tarayya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China