Taron cikniki da raya kasa na MDD ya ba da wani rahoto kan ''Jarin da aka zuba a duniya a shekarar 2013'' a ran 26 ga wata cewa, a cikin shekarar 2012, yawan jarin da aka zuba a duniya wato ma'aunin FDI ya ragu da kashi 18 cikin dari bisa na shekarar 2011. Rahoton ya ce, saboda tattalin arzikin duniya na fuskantar halin koma baya da rashin tabbaci, ana bukatar tsawon lokaci wajen farfadowar wannan ma'auni.
Rahoton kuma ya yi gargadi cewa, sauya shekar tsarin hada-hadar kudi na duniya, tsanantar halin tattalin arziki da ake ciki, da rashin tabbaci kan wasu manfufofi a wannan fanni, mai yiwuwa ne za su kara haddasa raguwar wannan ma'auni.
Ban da haka, rahoton ya bayyana cewa, a shekarar 2012, ko da yake FDI na kasashe masu tasowa ya ragu da kashi 4 cikin dari bisa na shekarar 2011, amma wannan ne karo na farko da adadin ya fi na kasashe masu wadata yawa, wanda ya kai kashi 52 cikin dari bisa dukkan adadin na duniya. (Amina)