in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
6 daga mafiya samun bunkasuwar tattalin arziki 15 a duniya tsakanin 2002 da 2012 suna Afirka
2013-05-31 14:44:54 cri

Shida daga cikin tattalin arziki goma sha biyar da nuna bunkasuwa mafi karfi a duniya, a tsawon lokacin shekarar 2002 da ta 2012, sun fito daga Afrika, a cewar wani rahoton gungun bankin cigaba Afrika (ADB) a wani labari da kamfanin dillancin labarai na MAP ya rawaito a ranar Alhamis.

Tare adadin bunkasuwar kayayyakin cikin gida (GDP) da kashi 6,6 cikin 100 a shekarar 2012, Afrika ta nuna babban karfinta na jurewa kalubalolin cikin gida da na waje, a cewar wannan rahoto da aka gabatar a yayin babban taron shekara-shekara na bankin ADB da aka gudanar a birnin Marrakech dake kudancin kasar Marocco.

Karuwar GDP ya samu kwarin gwiwa daga karuwar farashin kayayyakin bukatun farko, karuwar kason kayayyakin da ake fitarwa da bukatun cikin gida, tare da kuma kyautatuwar tsarin tafiyar da harkokin tattalin arziki, in ji bankin ADB, abun da ya bayyana bunkasuwa da kashi 8,7 cikin 100 a cikin kasashen dake fitar da man fetur a shekarar 2012, bisa ga kashi 3,9 cikin 100 na shigo da man fetur.

A game da sarrafa tattalin arzikin Afrika, bankin ADB ya bukaci da a fuskanci matsalolin dake da nasaba da kayayyakin aiki da tsarin dokoki dake kawo kalubale ga dunkulewar tattalin arziki a cikin gida da waje, tabbatar da aiwatar da manufofi masu fada a ji daka da hangen gaba, da samun bunkasuwar hadin gwiwa da za ta taimakawa kyautatuwar sarrafawa da ba da karfi ga kirkire-kirkire da shiga takara.

Game da bangarorin sarrafawa, sun shafi musammun ma bunkasa noma, sauya kwararowar harkokin musanya da jarin dake fita da kuma shigowa a nahiyar Afrika, bunkasa zuba jarin masu zaman kansu, zuba jari kan fasahohin zamani da sadarwa na TIC da kuma daidaita gibin gine-gine, a cewar bankin ADB.

Wakilai fiye da 3300 da suka fito daga kasashen duniya 78, suka halarci wannan taron shekara shekara na ADB, wanda ya kasance wata babbar dama ta tattaunawa kan muhimman batutuwa na Afrika dake shafar manyan manufofin aikin bankin ADB a shekaru goma masu zuwa wajen mai da hankali kan bunkasuwar tattalin arziki, samun bunkasuwa bisa girmama muhalli da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China