Shugabanni da manyan jami'ai na kasashe da yankuna 78, wakilan hukumomi kasa da kasa, da kwararru a fannin tattalin arziki da hada-hadar kudi, gaba daya mutane fiye da 3000 sun halarci wannan taro na yini 5, inda suka tattauna batun sauyawar tsarin tattalin arzikin kasashen Afirka.
Bankin raya nahiyar Afirka ya sanar da cewa, tattalin arziki nahiyar yana karuwa, inda yawan karuwar zai kai kashi 4.8% a shekarar 2013, da kashi 5.3% a shekarar 2014. Sa'an nan a wasu kasashe 9 dake nahiyar Afirka, wadanda suka fi samun karuwar tattalin arziki, za a gano wata karuwar da ta wuce kashi 7%.
A cewar bankin, tattalin arzkin nahiyar Afirka ya samun wannan ci gaba ne a sabili da hauhawar farashin danyen kayayyaki, samun karin zuba jari daga kasashen waje, karuwar yawan kayayyakin da ake fitowa da habakar bukatun gida. Har ila yau, cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen Afirka ita ma tana samun ci gaba, ta hakan kasashen nahiyar na kara samun karfin tinkarar sauyawar yanayi kan tattalin arzikin kasashen waje.(Bello Wang)