Mahukunta a Nigeria sun bayyana rashin gamsuwa da yanayin gudanar harkokin kasuwanci tsakanin kasar da takwararta wato kasar Rasha, a cewar jakadan Nigeria a kasar ta Rasha Mr. Assam Assam, ya ce, Rashan ce ta fi cin moriyarsa. Assam ya bayyana hakan ne a Jihar Akwa Ibom ranar Lahadin da ta gabata, yana mai alkawarta kokarin da ofishin jakadancin Nigeria a Rasha zai yi wajen samar da daidaito a wannan fanni, ta yadda za a janyo hankulan cibiyoyin kasuwancin Rasha zuwa harkokin cinikayyar albarkatun mai da iskar gas dake akwai a yankin Niger Delta.
A cewar jakadan Nigeria Assam Assam, rashin daidaito dake wanzuwa a wannan fanni na hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ya kai matakin da a shekarar bana Rasha ta shigar da kayayyaki Nigeria, da kimarsu ta kai dalar Amurka miliyan 350, yayin da ita kuma Nigeria ba ta samu damar fidda komai zuwa Rasha ba. Don haka jakadan ya ce, ofishinsa zai duba karin damar cin gajiyar huldar kasuwanci, musamman a fannoni da ba na mai ba. Tuni ma dai kasashen biyu, a cewar Mr. Assam, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin Gazprom na kasar ta Rasha, yarjejeniyar da aiwatar da ita, zai taimaka matuka wajen cin moriyar juna ta fuskar kasuwanci, da ma inganta huldar diplomasiyya tsakaninsu.(Saminu)