in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bukin tallata al'adun kasar Sin a makarantun sakandare dake Abuja
2013-03-27 15:01:05 cri






Ranar talata 26 ga wata, a makarantar sakandare dake unguwar Wuse 1 a birnin Abuja, tarayyar Najeriya, aka yi gagarumin bikin tallata al'adun kasar Sin na shekara ta 2013.

Babban jami'in kula da harkokin al'adu a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, Mista Jin Hongyue, darektan kwamitin kula da bada ilimi na tushe na birnin Abuja dokta Adamu Jato Noma, da dalibai da malamai sama da dari 4 na makarantu 20 ne suka halarci bukin. Jakadan kasar Sin dake Najeriya Mista Deng Boqing ya mika sako ga wannan buki, inda ya taya murnar gudanar da bikin cikin nasara.

Deng Boqing ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya na samun ci gaba kwarai da gaske, musamman ma a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu, ilmi da sauransu.

Ya ce, kasashen Sin da Najeriya na da abubuwa da dama kusan iri daya, dukkansu suna da dogon tarihi da kuma nagartattun al'adun gargajiya, kuma al'ummar kasashen biyu na son kara kyautata zaman rayuwarsu ta hanyar yin kokari. Jakada Deng ya yi imanin cewa, ta hanyar karfafa hadin-gwiwa da mu'amala ta fuskar al'adu, zai sa huldar dake tsakanin kasashen biyu ta kara inganta.

A wajen bikin, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya ba da kyautar kudi naira dubu dari uku ga kwamitin kula da bada ilimin tushe na Abuja, da kuma kyautar litttattafai, riguna, TV, da sauran wasu na'urorin aikin koyarwa ga makarantun wurin.

Shugabar makarantar sakandare ta unguwar Wuse 1 dake birnin Abuja Hajiya Adama Abdullahi Suleiman ta nuna godiya ga kyaututtukan da ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya bayar.

Bisa labarin da muka samu, an ce, za'a shafe tsawon kwanaki biyu ana yin bikin tallata al'adun kasar Sin cikin makarantun Abuja a wannan karo. Ranar 27 ga wata ne, aka nuna wasu fina-finan kasar Sin a makarantar sakandare ta unguwar Wuse 1.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China