Da farko dai, Wang Yang yi isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang zuwa ga Haile Mariam Desalegne, sannan ya ce, ya kamata, Sin da Afrika sun hara hadin gwiwa tsakaninsu a dukkan fannoni.
A nasa bangaren kuwa Haile Mariam Desalegne ya yi maraba da zuwan Wang Yang tare kuma da yabawa taimakon da Sin take bayar wa wajen raya kasar Habasha har ma da kasashen Afrika, yana fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban-daban. (Amina)