A jiya Lahadi 19 ga wata, aka bude taron koli na AU karo na 21 a garin Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.
An kira wannan taro na musamman ne da zummar bikin cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar hada kan nahiyar Afrika OAU wacce ta kasance tsohuwar kungiyar AU. Taron ya ci gaba da amfani da jigon da aka taba yi wato "Pan-Afirka da farfado da nahiyar Afrika". Kuma a lokacin taron, AU za ta gudanar da bikin cika shekaru 50 da kafuwar OAU.
A bikin bude taron da aka yi a wanann rana, Shugaban AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna cewa, jerin ayyuka da za a yi yayin taron da zummar sa kaimi ga jama'ar Afrika da su tuna da baya da kuma hangen hasken gobe, kara musu kwarin gwiwar shiga ayyukan farfado da Afrika da kuma samar da wani yanayi mai kyau nan gaba a Afrika. A wannan rana, tun farko an yi taron kwamitin wakilan dindindin karo na 26 na tsawon kwanaki biyu, daga baya kuwa, za a kira taron majalisar zartaswa ta ministocin harkokin waje na mambobin kasashen AU da taron shugabannin kasashen AU.
Shugabannin kasashe da na gwamnatoci kimanin 75 na Afirka da sauran kasashen duniya za su halarci taron koli ko ragowar bukukuwa. A lokacin ne wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mataimakin firaministan kasar Wang Yang zai halarci bukukuwan da abin ya shafa. (Amina)