A jiya Alhamis 23 ga wata a birnin Addis Ababa hedkwatar kasar Habasha, mataimakin shugaban kwamitin AU Erastus J.O. Mwencha ya bayyana cewa, kungiyar na yin iyakacin kokarin samun hanyoyi masu kyau wajen tattara kudi tare kuma da dukufa kan tafiyar da aikin kasafin kudi da kanta. Idan za a iya cimma wannan buri, AU za ta kawar da wata babbar wahala da aka dade ana fama da ita na karancin kudi.
Erastus J.O. Mwencha ya ce, kungiyar AU ta kan dogaro da abokanta na kasashen waje a kan wannan batu, amma yanzu wannan hanyar da take bi tana fuskantar kalubale mai tsanani.
Erastus J.O. Mwencha ya kara da cewa, abokan kasashen yamma ba za su iya cika alkawarinsu ba saboda wasu dalilai da suka hada da matsalar hada-hadar kudi da sauransu, abin da ya sa AU ta gagara samun isasshen kudi domin samun tabbaci ga ayyukanta. Saboda haka, AU ta kara hadin gwiwa da wasu kasashe masu saurin bunkasuwa ciki hadda kasar Sin domin kawo moriyar juna. Yana mai cewa, kasashen Afrika za su taka rawarsu domin cimma burinsu na zama mihimmin mafarin samar da kudi ga kungiyar AU a karshe.
A halin yanzu, kasafin kudin da kungiyar AU ke tafiyar da shi ya zo ne musamman daga hanyoyi 2, ta farko, kudin da ya ba da tabbaci ga ayyukan da hukumominta za su gudana, mambobin kasashen AU ne suke samar da wadannan kudi da kansu. Ta biyu kuwa, kudin da AU take bukata domin tafiyar da ayyukata a ko wace shekara, yawancinsu AU ta tattara su ne daga abokanta na kasashen ketare, wanda yawansu ya kai kashi 42 cikin dari. Bisa kididdigar da AU ta bayar, Afrika na bukatar a kalla dala biliyan 60 a cikin shekaru goma masu zuwa domin aiwatar da manyan ababen more rayuwa. Amma, kasafin kudi da AU ta yi a shekarar 2013 ya kai dala miliyan 308 kawai, yayin da wannan adadi na EU ya kai kudi Euro biliyan 140. (Amina)