A lokacin ganawar, Wang Yang ya ce, kafuwar wannan kungiya ya amfana ma kasashen Afrika wajen samun 'yanci, hadin gwiwa, kwanciyar hankali da wadata, sannan ya taka rawa wajen daga matsayin kasashen Afrika a duniya don haka kasar Sin na fatan kasashe da jama'ar Afrika su yi amfani da zarafi mai kyau yanzu domin kara sa kaimi ga ra'ayin Pan-Afrika, da samun bunkasuwa cikin lumana yadda ya kamata.
A nata bangaren Madam Nkosozana Dlamini-Zuma ta bukaci Wang Yang da ya isar da godiya da gaisuwarta zuwa ga Shugaba Xi Jinping, tare kuma da yin maraba da zuwan Wang Yang domin halartar wannan taro na musamman, sannan kuma tana fatan kara hadin kai da kasar Sin a fannoni daban-daban. (Amina)