in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Korea ta arewa ta harba wasu makamai masu linzami masu cin gajeren zango, in ji kamfanin dillancin labaru na Korea ta kudu
2013-05-20 15:20:25 cri

Kamfanin dillancin labaru na Korea ta kudu ya ruwaito maganar sojin kasar a ran 19 ga wata cewa, Korea ta arewa ta harba wani makami mai linzami mai cin gajeren zango a wannan rana da yamma daga gabashin sararin tekunta zuwa ga wurin dake arewa maso gabas, wannan ya kasance makami na hudu da Korea ta arewa ta harba a cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Hukumar soja ta Korea ta Kudu ta ba da labari cewa, a ranar 18 ga wata, kasar Koriya ta arewa ta harba makamai masu linzami har sau uku daga gabashin sararin tekunta zuwa wurin dake arewa maso gabas, daga cikinsu, sau biyu a safiyar wannan rana, saura guda kuma a yamamcin wannan rana.

Har yanzu Korea ta arewa ba ta ba da labari game da makamai masu linzami da ta harba cikin kwanakin nan biyu ba tukuna.

A wannan rana, ma'aikatar hadin kan kasar Korea ta kudu ta ba da wata sanarwar yin Allah wadai da aikin da Korea ta arewa ta yi.

Kakakin kwamitin tsaron kasar Amurka na White House Caitlin Hayden a cikin wani sakon E-Mail da ya baiwa manema labaru ya nuna cewa, matakin da Korea ta arewa ta dauka ya kara mai da ita saniyar ware ke nan tare kuma da kawo cikas ga kokarin da kasa da kasa ke yi a yankin arewa maso gabashin Asiya domin shimfidar zaman lafiya da karko.

Ban Ki-Moon babban sakataren MDD wanda ke yin ziyara a kasar Rasha ya nuna damuwa sosai ga wannan al'amari a ran 19 ga wata a birnin Moscow, kuma ya yi kira ga Korea ta arewa da ta sassauta halin da ake ciki tare kuma da komawa teburin yin shawarwari tsakanin bangarori 6. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China