Kakakin fadar shugaban kasar Amurka Jay Carney ya fadi a ran 9 ga wata cewa, yadda a wannan rana Korea ta arewa ta yi kira da 'yan kasashen ketare dake zaune a Korea ta kudu, da su dauki matakan da suka dace, domin kauracewa gamuwa da hadari, zai iya tsananta halin da ake ciki a zirin Korea.
A gun taron manema labaru da aka saba yi, Jay Carney ya yi kira ga shugabannin Korea ta arewa, da su bi hanyar zaman lafiya tare da daukar nauyin dake wuyansu. Ban da haka, a cewarsa, Amurka na daukar matakin da ya dace da nata matsayi.
A wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Rasha Mr Sergei Lavrov, ya shaidawa manema labaru cewa, a matsayinta na mambar MDD, yadda Korea ta arewa ta sabawa kudurorin da majalisar ta yanke abu ne da ba za a yarda ba. A ganinsa, gudanar da dukkanin aikin gwaji nukiliya, ko makamai masu linzami zai tsananta halin da ake ciki. Dadin dadawa, tankiya da bangarori daban-daban da abin ya shafa suke yi, za ta kawo illa matuka da gaske. Kasar Rasha za ta ci gaba da ba da taimako wajen sassauta halin da ake ciki a zirin, tare da kalubalantar bangarori daban-daban, da su koma ga shawarwarin bangarorin nan shida da aka gudanar a baya.
Hakazalika, a wannan rana, wani babban jami'i mai kula da harkokin Asiya na kungiyar EU ya fadi cewa, kungiyar za ta mai da hankali sosai kan yanayin da wannan yanki ke ciki, tare da kara sanya takunkumi, muddin Korea ta arewa ta sake harba makamai masu linzami, ko ta gudanar da aikin gwajin nukiliya. (Amina)