A cewar ministan harkokin wajen kasar Sin, Koriya ta Arewa ta yi fatali da kin amincewar da gamayyar kasa da kasa suka yi, inda ta sake gwajin fasahar samar da makaman kare dangi na nukiliya. Kasar Sin ta nuna rashin gamsuwa da cikakkiyar kiyayya kan wannan batu.
Minista Yang ya kara da cewa, kasar Sin ta dade tana kiran cewa a kau da makaman nukiliya daga zirin Koriya, don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a wurin. Sa'an nan kasar ta ga ya kamata a daidaita sabanin dake tsakanin bangarori daban daban ta hanyar shawarwari, musamman ma bisa tsarin shawarwari da ya shafi bangarori 6. Don haka Yang ya bukaci Koriya ta Arewa da ta daina ayyukan ta da kayar baya, kana ta dawo teburin shawarwari wanda shi ne madaidaiciyar hanya.
A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ba da sanarwa a ranar Talata cewa, kasar Sin ba ta amince da sabon gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi kwata kwata.(Bello Wang)