in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri dangane da gwajin nukiliya a kasar Korea ta Arewa
2013-03-08 14:51:19 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri mai lamba 2094 a ran 7 ga wata game da gwajin nukiliya karo na uku a kasar Korea ta Arewa. Wannan kuduri ya nemi kasar Korea ta arewa da ta dakatar da yin irin wannan gwaji tare kuma da yin watsi da shirin raya makaman nukiliya, kana ta sake shiga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

Ban da haka, kudurin kuma ya amince da warware wannan batu ta hanyar diplomasiyya da siyasa cikin lumana, tare kuma da nanata wajibcin farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida.

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa cewa, matakin da kwamitin ya dauka na nunawa Korea ta arewa wani muhimmin alama ce cewar, ko kadan kasashen duniya ba za su yarda Korea ta arewa ta raya sha'anin makaman nukiliya da ma sauran ayyukan da suka shafi wannan batu ba.

A sa'i daya kuma, ya bayyana matsayin da kwamitin ke dauka na yaki da gwajin nukiliya da kiyaye zaman doka a duniya da kuma hana yaduwar makaman nukiliya.

Kakakin fadar shugaban kasar Amurka ta White House Carney ya nuna a gun wani taron manema labaru cewa, kasashen duniya sun cimma matsaya daya kan tabbatar da alkawarin kawar da makaman nukiliya a zirin Korea da kuma neman Korea ta arewa da ta aiwatar da hakkinta kan harkokin kasashen duniya.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha ita ma ta ba da sanarwa cewa, kasar na fatan Korea ta arewa za ta fahimci kudurin da aka bayar, da kuma yin watsi da shirin yin bincike da kuma kera sabbin makaman nukiliya.

Bugu da kari, kasar Rasha na fatan ganin bangarori daban-daban za su kauracewar daukar matakai da ka iya tsananta da halin da ake ciki a zirin Korea da yankin arewa maso gabashin Asiya.

Yayin da kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang yake amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa ya ce, Sin na goyon baya matakin da ya dace da kwamitin sulhu ya dauka kan gwajin nukiliya da Korea ta arewa ke yi, aikin kiyaye zaman lafiya da karko a zirin Korea da yankin arewa maso gabashin Asiya ya dace da moriyar kasa da kasa.

Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa da su yi sulhu bisa tsarin shawarwarin tsakanin bangarorin shida, tare kuma da samar da wata hanya da ta dace wajen tabbatar da zaman oda da doka cikin dogon lokaci a zirin Korea da yankin arewa maso gabashin Asiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China