Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya buga wayar tarho ga takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, inda jami'an biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan gwajin nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta yi, kana da halin da zirin koriya ke ciki yanzu. Haka kuma sun amince da tuntubar juna a kowane lokaci a kan batun.(Kande Gao)