Bayan da kamfanin dillancin labarun kasar Koriya ta Arewa KCNA ya sanar da nasarar da kasar ta samu wajen gwajin makaman nukiliya karo na 3 a ranar Talata 12 ga wata, kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa inda ya yi Allah wadai da lamarin da babbar murya.
A ranar Talata da safe, kwamitin sulhun ya kira taron gaggawa, daga bisani ya sanar da cewa yana Allah wadai da gwajin nukiliyan karo na 3 da Koriya ta Arewa ta yi. An ce lamarin ya sabawa kudurorin kwamitin, don haka mambobin kwamitin za su fara tattaunawa don mayar da martani, wanda zai kasance wani sabon kudurin kwamitin.
A wannan rana kuma, Ban Ki-moon, babban sakataren MDD shi ma ya yi tir da sabon matakin gwajin nukiliya da Koriya ta Arewa ta dauka, yana mai cewa abin da kasar ta yi ya keta kudurorin kwamitin sulhun MDD a zahiri.
A nasu bangaren, Barrack Obama, shugban kasar Amurka, da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Lee Myong-pak sun la'anci matakin gwajin nukiliya na Koriya ta Arewa a ranar Talata, kana shugaba Obama ya nanata alkawarin da Amurka ta yi wa Koriya ta Kudu wajen tabbatar da tsaron kasar, abin da ya shafi laimar tsaro da Amurka ta samar ta makaman nukiliya da ta mallaka.
Haka zalika, kungiyar hana yaduwar makaman nukiliya ta CNTBTO ta ba da labari a ranar 12 ga wata cewa, bisa alkaluman da aka samu yanzu, karfin makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi gwajinsa a wannan rana ya ninka makamin da ta yi gwajinsa a shekarar 2009 har sau 2. (Bello Wang)