Sabbin takunkumin da za a saka wa Koriya ta Arewa sun kunshi abubuwan da ke cikin kuduri mai lamba 2087 da kwamitin sulhu na M.D.D ya fitar, wato wanda ya hada da hana jami'an gwamnatin Koriya ta Arewa da su yi tafiya, da kuma hana amfani da kaddarori na kasar Koriya ta Arewa. Ban da wannan, kungiyar EU ita ma da kanta, ta hana fitar da na'urorin yin rokoki zuwa kasar Koriya ta Arewa, da hana musayar hannayen jari, da zinariya, da albarkatun ma'adinai, da lu'u-lu'u a Koriya ta Arewa, kana kuma, an hana bankin Koriya ta Arewa da ya bude sabon reshe a kasashen kungiyar EU ko ya yi hadin gwiwa da hukumomin kudi na kungiyar EU, hakazalika an hana bankunan kungiyar EU da su bude rassan bankuna a kasar Koriya ta Arewa.
A cikin sanarwar taron ministocin harkokin waje na kasashen 27 na kungiyar EU, an ce, kungiyar EU za ta ci gaba da yin shawarwari da manyan abokanta, don ci gaba da nazarin sabbin takunkumi da za a saka wa kasar.(Bako)