Dangane da hakan ne kuma kasar Iran wacce ta zamo kasa da kowa ke mai da hankali kanta saboda wannan batu, ta mayar da martani cewa, bai kamata kowace kasa ta gwada makaman nukiliya a kokarin cimma burinta na aikin soja ba.
A ran 12 ga wata, yayin da yake ba da amsa na tambayar da 'yan jarida suka masa kan gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran, Mechman Palasite ya bayyana cewa, bai kamata kowace kasa ta gwada makaman nukiliya don kawai ta cimma burinta na aikin soja ba.
Yace dole ne a lalata dukkan makaman nukiliya, kuma kowace kasa na da ikon amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. Ya ci gaba da cewa kamata ya yi wasu manyan kasashe dake kashe makudan kudade domin cika dakinsu na ajiye makamai da makaman nukiliya, su rage yawan irin wadannan makaman da suka mallaka tukuna.
Dadin dadawa, Mechman Palasite ya kara da cewa, Iran memba ce ta kungiyar IAEA, wadda ta rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da yaduwar makaman nukiliya, tare da cika alkawarinta kan haka.
Game da batun sansanin soja na Parchin da kasa da kasa ke mai da hankali a kai, Palasite ya furta cewa, an yi bincike kan sansanin sau biyu, bayan da Iran ta hada gwiwa da kungiyar IAEA, kuma ana sa ran cewa, bangarorin biyu za su cimma matsaya kan batun sake yin bincike a wannan sansani.(Fatima)