Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Koriya ta Arewa KCNA ya bayar a ranar Talata 12 ga wata, an ce, kasar ta cimma nasarar gwajin makaman nukiliya a karkashin kasa a karo na uku.
Labarin ya ce, an tabbatar da cewa, wannan gwaji yana da karfi sosai, kuma yana kan matsayin koli mai tsaro sosai, wanda ba zai yi illa ga halittu da muhallin dake kewaye da shi ba.
Haka kuma labarin ya ce, Koriya ta Arewa ta gwada makaman nukiliyar ne domin mai da martani ga danyen aikin da Amurka ta yi na keta hakkin kasar na harba tauraron dan adam bisa dokoki cikin lumana.
A game da wannan batu, kasa da kasa sun mai da martani a kai a kai.
A wannan rana, babban sakataren mai kula da diplomasiyya da tsaro na shugaban kasar Koriya ta Kudu, Chun Yung-woo ya ba da sanarwar cewa, bayan harba roka, Koriya ta Arewa ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya ba bisa yardar kowa ba, wannan ya keta kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 1874 da 2087. Kuma wannan gwajin zai yi barazana ga zaman lafiya da tsaro na zirin Koriya, har ma ga arewa maso gabashin nahiyar Asiya baki daya, sannan kuma wannan takala ce da Koriya ta Arewa take yi ga duniya baki daya.
A yammacin wannan rana, shugaba mai jiran gado ta kasar Koriya ta Kudu, Park Geun-hye ta ba da sanarwar yin Allah wadai da gwajin makaman nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta yi karo na uku.
Ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu tana ganin cewa, watakila kasar Koriya ta Arewa za ta sake gwajin makaman nukiliya, ko harba makamai masu linzami. A sakamakon haka, sojojin Koriya ta Kudu da sojojin Amurka dake wurin zasu kara sa ido akan Koriya ta Arewa.
Bugu da kari, a wannan rana, shugaban kasar Japan, Shinzo Abe ya yi shelar cewa, Japan za ta dauki kowane irin matakai domin tinkarar batun gwajin makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi, ciki har da kakaba mata takunkumi da kanta.
Bayan wannan kuma, an gudanar da taron tabbatar da tsaro cikin gaggawa a fadar shugaban kasar Japan, tare da canza ofishin ba da sakwannin sirri na majalisar ministocin kasar da aka kafa domin tinkarar batun zirin Koriya, zuwa ofishin tinkarar matsaloli na fadar shugaban kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, kwamitin sulhu na MDD zai kira wani taro cikin gaggawa a daren ranar 12 ga wata da misalin karfe 22 bisa agogon birnin Beijing, inda za a yi shawarwari kan batun gwajin makaman nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ta yi.
A nasa bangare, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi Allah wadai da wannan gwajin makaman nukiliya. Ya ce wannan takala ce da Koriya ta Arewa take yi ga kasa da kasa, tare da kalubalantar kasashen duniya su dauki matakai masu amfani cikin sauri domin daidaita wannan batu.(Fatima)