in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Korea ta arewa na yin shirin harba makamai masu linzami
2013-03-29 16:56:38 cri

Yau Jumma'a 29 ga wata da safe, shugaban Korea ta arewa Kim Jong-un ya kira wani taro cikin gaggawa, domin shirin harba makamai masu linzami saboda ganin cewa, kasar Amurka ta tura jiragen saman yaki masu bacewa samfurin B-2 zuwa Korea ta kudu don yin rawar daji.

An ba da labari cewa, Amurka ta yi biris da gargadi da Korea ta arewa ta bayar sau da dama, har ta yi atisaye a fili don kai hari kan takitocin dake kasar Korea ta arewa.

A ganin Kim Jong-un, matakin da Amurka ta dauka ya kasance matsin lamba ne na yin amfani da karfin tuwo a kan Korea ta arewa, inda har ya ba da gargadin karshe cewa, Amurka za ta tada yaki a zirin Korea. Rundunar Korea ta arewa za ta mayar da martani mai tsanani wato za ta yi yaki mai adalci daga duk fannoni kan barazanar nukiliya da Amurka ta yi mata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China