A lokacin wannan waya tasu,Shugabannin biyu sun amince da daukan mataki a kan kasar Koriya ta Arewa sannan kuma zasu hada kai da MDD wajen neman sabuwar matsaya a kan kasar,kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Japan Kyodo ta sanar.
Duka bangarorin biyu sun kuma amince da Japan,Amurka da kuma Koriya ta Arewa ya kamata su yi aiki kafada da kafada a game da wannan al'amari,in ji Kyodo wadda ta ambato wani jami'in kasar Japan da fadin haka.
Abe ya shaida ma Obama cewa gwajin da Koriya ta Arewa ta yi zagon kasa ne ga samar da zaman lafiya na kasa da kasa don haka wannan ya jawo bukatar da ke akwai ga Japan da Amurka suma su kakaba nasu takunkumin a kasar Koriyar ta Arewa.
A nashi bangaren Obama yace Amurka a shirye take ta kare kasar Japan.
A ranar laraba,Japan,Koriya ta kudu sun yarda da neman kwamitin sulhu na MDD data sanya takunkumi mai karfi a kan Koriya ta Arewa.
Haka kuma a lokacin zantawar su ta wayan tarho,Firaministan Japan Abe da Shugaban koriya ta kudu Lee Myung –Bak sun amince da cewa ya kamata kwamitin tsaro na MDD ta dauki tsauraran mataki akan Koriya ta Arewa tare da bada tabbacin cewa kasashen su zasu bada goyon bayan da ya kamata don ganin hakan ya tabbata. (Fatimah Inuwa Jibril)