in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in wanzar da zaman lafiya na MDD ya bukaci daidaita matsalar rikicin Darfur ta hanyar siyasa
2013-04-30 16:36:23 cri
Jagoran jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a jiya litinin 29 ga wata ya yi kira ga kasashen duniya da su yi matsin lamba a kan bangarorin da rikicin yankin Darfur na kasar Sudan ya shafa da su cimma yarjejeniya ta hanyar siyasa, yana mai cewa aiwatar da aikin soji ba shi ne mafita ba.

Herve Ladsous wanda shine mataimakin babban magatakardar MDD a bangaren wanzar da zaman lafiya lokacin da yake bayanin a taron kwamitin sulhun game da ayyukan tawagar da kungiyar tarayyar kasashen Afrika(AU) da MDD suka tura a yankunan da ake fuskantar tashin hankali na yammacin yankin Sudan UNAMID, ya ce akwai matukar damuwa game da halin da ake ciki.

Mr Ladsous ya yi wannan bayanin ne sakamakon wani mummunan tashin hankalin da ya sake barkewa tsakanin kabilu a yankin na Darfur abinda ya kawo daukar matakan tsaro na walwala kuma ya haifar da cikas ga ayyukan jami'an tsaro na MDD da AU.

Yace warware wannan tashin hankali ya shafi ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen da ke wakilci a wannan kwamitin sulhu su 15,kungiyar tarayyar kasashen Afrika,AU,da kuma sauran al'ummomi a ko'ina da zasu iya bada taimakon da za'a ga cewar bangarorin da wannan abu ya shafa sun koma kan teburin shawarwari domin sulhu,saboda amfani da karfin soja ba shi ne mafita ba,kuma yana da imanin cewa dole ne a maida hankali sosai a kan wannan yanki ganin yadda sabbin rigingimu ke bullowa.

Mr Ladsous yace har yanzu ba a samar da wani yarjejeniyar da za'a fitar da wani tsari a siyasance ba duk da ana ba da kwarin giwa ga cigaban ayyukan samar da zaman lafiya.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China