in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata babbar jami'ar AU ta yi fatan kafofin watsa labarai za su taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da hadin gwiwar Sin da Afirka gaba
2012-08-09 11:43:06 cri

Shugabar rikon kwaryar hukumar AU, Dr. Elham Mahmoud Ahmed Ibrahim, ta fada a ranar Laraba a Addis Ababa yayin da take ganawa da He Ping, babban editan kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a hedkwatar AU cewa, kungiyar AU za ta kara bunkasa dangantakar abokantaka da Sin, kana ta ciyar da dangantaka tsakanin kafofin watsa labaran Afirka da na Sin, ciki har da Xinhua gaba.

Elham ta shaidawa He Ping cewa, kungiyar AU ta tsara wasu matakai guda 3 na bunkasa tattalin arzikin Afirka tsakanin shekara ta 2012 da 2040, da jarin da ya kai dala biliyan 360.

Ta ce, yayin da Sin ke kasancewa muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar Afirka a bangaren tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar, ana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a nahiyar.

He Ping ya ce, shugaba Hu Jintao na kasar Sin, ya fada a yayin taron ministoci karo na biyar na dandalin FOCAC cewa, muddin ana bukatar a cimma sabbin nasarori cikin sabon tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka, kamata ya yi bangarorin biyu su kara musayar al'adu da al'ummomi, kara tuntuba tsakanin kafofin watsa labarai, ta yadda za a samar da fasahohi da tallafin al'adu a huldar da ke tsakanin sassan biyu.

A wani labarin kuma, shugaba Girma Wolde-Giorgis na kasar Habasha, ya fada a ranar Laraba cewa, kasar Habasha a shirya take ta zurfafa huldar dangantakar abokantaka da Sin.

Shugaba Girma ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da He Ping, babban editan kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a fadar shugaban kasar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar.

Girma ya ce, Sin ta taimakawa Habasha a fannonin jin dadin rayuwar jama'a, ci gaban tattalin arziki, rage talauci, kuma Habasha tana son kara inganta huldar abokantaka da Sin tare da kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A jawabinsa He Ping ya ce, yana fatan al'ummomin sassan biyu, za su taimakawa wajen kara bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Habasha.

Ya ce, yana farin cikin ganin yadda tattalin arzikin kasar Habasha ke bunkasa cikin sauri a 'yan shekarun nan, duk da matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China