A ranar Litinin ne ministocin harkokin waje da manyan jami'an gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar hadin kan kasashen Afirka suka hallara a hedkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, don yin ganawa ta musamman karo na 14, na majalisar zartaswar kungiyar.
An kira wannan taro ne don tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi bikin cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar hada kan kasashen Afirka wacce a baya ake kira OAU, a yanzu kuma AU.
Ministocin har wa yau za su amince da tsarin hukumar gudanarwar kungiyar na shekarar 2014 zuwa 2017 wacce ke da tasiri ga cimma hadin kai, wadata da kuma zaman lafiya a nahiyar baki daya.
A cikin jawabinta na bude taron, shugabar hukumar gudanar da kungiyar AU, Dlamini Zuma ta bayyana cewa, wajibi ne bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar ya zamo wata kyakkyawar damar jan hankalin 'yan Afirka baki daya har da wadanda suke wajen nahiyar dangane da buri da nahiyar ke da shi na cimma hadin kai, bunkasa da kuma zaman lafiya.
A yayin da yake jagorantar taron majalisar zartaswar karo na farko bayan hayewar kasarsa kujerar mukamin shugabar kungiyar, watanni biyu da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Habasha, Tewodros Adhanom, ya ce, tsarin kungiyar AU na shekarar 2014 zuwa 2017, wanda shi ne na uku, ya dau darussa daga nasarori da aka cimma da kuma kalubale da aka fuskanta wajen aiwatar da tsarin kungiyar na baya, guda biyu.
Ministan ya ci gaba da cewa, ya dace wannan sabon tsari ya sama mana matashiya mai inganci, wacce za ta haifar da alkibla mai kyakkyawar makoma domin a iya aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su kawo canji mai ma'ana a rayuwar jama'armu.(Lami)