Kwamnishinan zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU Ramtane Lamamra,shi ne ya bayyana wannan bukatar a lokacin da ake taron kungiyar tarayyar kasashen BRICS a kasar Afrikan ta kudu..
A ganawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce akwai bukatar haduwa gu daya a tsaida maganar yadda za'a shawo kan wannan matsala ta kasar Afrika ta tsakiya sannan kuma har ila yau akwai bukatar a mara ma kasar baya domin ta maido da doka da oda. (Fatimah Jibril)