Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta gabatar a ranar Laraba wani shirin hadin gwiwa dake da manufar rage yawan asarar albarkatun noma da ake samu bayan damina a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, wannan kuma tare da taimakon kungiyar abinci da noma (FAO).
A yayin wani zaman taro na kwanaki biyu bisa wannan shiri a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, kungiyar AU ta bayyana cewa, wannan dandali da tattara masu fada a ji a fagen siyasa da kuma masu ruwa da tsaki a fannin noma wajen karfafa aiwatar da babban tsarin bunkasa aikin noma a nahiyar Afrika (CAADP).
Sakamakon shekarar 2011 na FAO da bankin duniya ya kimanta cewa, yawan asarar hatsi da makamantan haka da ake samu bayan damina a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara ya kai dalar Amurka biliyan hudu, kudaden ke iyar taimakawa sosai wajen biyan bukatun shekara guda na mutane miliyan 48. Domin magance wannan matsala, kungiyar AU tare da hadin gwiwar kungiyar FAO ta kirkiro wannan shiri da za'a aiwatar a tsawon watanni 18. Kuma wannan shiri ya shafi gina wuraren adano, samar da dokoki da kuma bunkasa zuba jari.
Darektan reshen tattalin arzikin karkara da noma na kungiyar AU, Yemi Akinbamijo ya bayyana cewa, asarar cimaka da ake samu na da yawa sosai kuma tana kara tsananta matsalar karancin abinci tare kuma da janyo barnar irin shuka, takin zamani, ruwa da wahalar aiki ga mutane. (Maman Ada)