Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta dauki niyyar bada hannu a ranar Alhamis ga tawagar zaman lafiya da matan shugabannin kasashen Afrika suka kafa, da ta bayyana cewa, za ta aiwatar da matakai da kudurorin dandali karo na bakwai na tawagar zaman lafiya ta matan shugabannin kasashen Afrika (AFLPM) da a yanzu haka ke gudanar a Abuja, hedkwatar tarayyar Najeriya.
Darektar kwamitin mata, jinsi da cigaba ta kungiyar AU Litha Musyimi-Ogana ta shaidawa manema labarai cewa, lokaci ya yi na daukar nagartattun matakai domin daidaita ayyukan dake jiran mu na tashe-tashen hankalin da shiyyar take fuskanta.
"Hakan zai taimaka wajen samun bunkasuwa a Afrika", in ji ta, tare da cewa, sanarwar shekarar 2010 zuwa 2020 a matsayin karnin matan Afrika ta AU dake bayyana cewa, ya kamata matan Afrika su kasance masu bada taimako ga yawan kokarin da ake yi na samun cigaba, musammun ma na gida.
Hakazalika ta bayyana cewa, matan Afrika sun tsintsi kansu cikin wani hali na matsi inda dole sai sun canja hanyar da za su bi a nahiyar, kana kuma a lokacin da matan shugabannin kasashen Afrika suka dauki niyyar gabatar da wadannan tambayoyi masu wuya, hakan ya taimaka wajen saukaka aikin kungiyar AU. (Maman Ada)