Uwargida Dlamini-Zuma na samun goyon baya daga gwamnatin kasar Afrika ta kudu da kuma kungiyar tattalin arziki da bunkasa kasashen kudancin Afrika ta SADC. Wadanda kuma ke ganin 'yar takarar ta cancanta, kamar yadda Maite Nkoana-Mashabane, ministar hulda da kasa da kasa ta kasar Afrika ta kudu, ta sanar a garin Pretoria.
Uwargida Dlamini -Zuma,'yar takarace da za ta kare darajar nahiyar baki daya , kamar yadda ka'idodin kungiyar tarrayar Afrika suka yi amana a kan matakai na siyasa, da kuma abun da taron manyan jami'ai ya tsayar. Ba wai tana takara ba ne, domin kare darajar wata kasa ba, ko kuma wani yankin ba, cewar Uwargida Nkoane -Mashabane.
Yankunan kudu da na arewaci ba su taba samun sukuni ba na jagorantar kwamitin kungiyar tarrayar Afrika, cewar Ministar.
Ta sanar da cewa, Unwargida Dlamini-Zuma na da bukatar goyon bayan kasashe masu magana da harshen Faransanci a game da wannan zabe. Yankin kuma zai ci gaba da gudanar da tattaunawa da dukkan bangarori na nahiyar a game da takarar Uwargida Dlamini- Zuma, kamar yadda ministar ta jadada. (Abdou Halilou)