Sanarwar ta bayyana cewa sarakunan gargajiya sun bukaci kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar ECOWAS, CEMAC, UEMOA da AU da su amince da kuma baiwa kungiyar sarakunan gargajiya na Afrika wani matsayi na 'yan kallo a yayin tarurukansu kan batutuwan rigakafin tashe tashen hankali a cikin shiyoyin da ma nahiyar baki daya, da kuma kebe ranar amincewa da matsayin sarakunan gargajiya da karfin ikonsu a cikin al'umomin Afrika.
Hakazalika sanarwar ta nuna cewa sarakunan gargajiya sun bukaci gwamnatocin Afrika dasu rika koyi da abubuwan tarihin gargajiya masu daraja da aka gada domin magance tashe tsahen hankali dake kamari a nahiyar Afrika duk da kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma demokuradiya, wadannan abubuwan tarihi masu daraja su ne gafartawa juna, tattaunawa da samun jituwa. (Maman Ada)