Kungiyar Tarayyar kasashen Afrika ta AU a ranar Talata ta tabbatar da wurin da za a gudanar da taron kungiyar na gaba. Taron da ya kamata a gudana a watan Juli a Lilongwe, babban birnin kasar Malawi, zai gudana a Addis Abeba, babban birnin kasar Habasha.
A cikin sanarwar da manema labarai suka samu, kungiyar ta AU ta sanar da cewa, babu wani canji da aka samu a game da ranar gudanar da taron daga 9 zuwa 16 ga watan Juli. Kuma taken taron shi ne bunkasa ciniki a cikin nahiyar Afrika.
A ranar 8 ga watan Yuni, mataimakin shugaban kasar Malawi, Khumbo Kachali ya sanar da cewa, kasar Malawi ba ta amincewa da shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al-Bashir da ya shiga taron bisa dalilin kotun kasa da kasa ta CPI ke nemansa.
A ranar Lahadin da ta gabata, a cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, shugaban kwamitin kungiyar ta AU Jean Ping ya sanar da cewa, taron na gaba zai gudana ne a hedkwatar kungiyar a Addis Ababa. Kuma kasar Malawi ta dauki wannan mataki ne sabili da matsin da take samu daga kotun kasa da kasa ta CPI.(Abdou Halilou)