in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS da CILSS sun kafa wani runbun tsimi domin magance matsalar karancin abinci
2012-12-18 14:07:47 cri

Hukumomin dake kula adano da tsaron cimaka a cikin kasashen yankin Sahel da yammacin Afrika (RESOGEST) sun kaddamar da wani shiri mai taken "runbun tsimi takwas" a kwanan nan domin bunkasa taimakon juna a lokacin da za'a gamu da karancin abinci a cikin wadannan yankuna biyu, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a ranar Litinin daga ma'aikatar noma.

Wannan runbun tsimi takwas ya kunshi kasashe takwas da suka tanadi karin rarar abinci bisa kasashe goma sha bakwai dake cikin kwamitin CILSS na kasashen yankin Sahel dake yaki da hamada da kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS).

Wadannan kasashe takwas su ne suka fi samun rarar abinci da kuma da kwarewa a fannin daidaita batutuwan gaggawa da suka shafi matsalar karancin abinci. Kafa wannan shiri na da nasaba da matsalolin da ake fuskanta na karancin abinci a cikin wasu kasashe dake cikin wannan yanki na CILSS da ECOWAS. A cikin wannan yanki, an fuskanci matsalar karancin abinci a damunar shekarar 2011 zuwa 2012 a cikin kasashe mafi yawa daga wannan yanki, lamarin da ya janyo barazanar rashin abinci. A cikin kasashe 17 dake yankin CILSS da ECOWAS, kasashe hudu wato Cote d'Ivoire, Benin, Nijeriya da Togo kawai suka samu karin abinci kuma su ne kasashen da ake dauka a matsayin runbun tsimi a wannan yanki idan aka fuskanci barazanar karancin abinci. (Maman Ada) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China