in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO za ta shirya taron koli don tinkarar rikicin hatsi da kasashen da ke kuriyar Afirka suka fuskatar
2011-08-18 16:59:27 cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Itallya ANSA ya bayar, an ce, hukumar FAO ta yanke shawarar cewar za ta bude taron koli a ran 18 ga wata, a birnin Rome, kuma babban jigon taron shi ne yin kira ga kasashen duniya da su kara mai da hankali a kan rikicin hatsi da kasashen da ke kuriyar Afirka suke fuskantar. Wakilan hukumomin M.D.D, ministocin kasashen Afirka da zu halarci taron, don tattauna kan halin rashin abinci da matakai da kasashen duniya za su dauka, da aiwatar da shirin ba da taimako.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, yawan yara wadanda suka mutu a sakamakon cutar kyanda da batun rashin abinci a ko wace rana a sansanin 'yan gudun hijira na kasar Habasha ya kai 10. Bisa labarin da babban jami'in hukumar UNHCR ya bayar, an ce, yanzu yawan yara da suke fama da rashin isasshen abinci mai gina jiki a kuriyar Afirka ya kai kusan miliyan 2 da rabi, kuma yawan mutanen da suke fuskantar karancin ruwan sha ya kai miliyan 12.4.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China