Manoma da masana'antun noma a Afrika na iyar kafa wata kasuwar abinci ta dalar Amurka biliyan dubu nan da shekarar 2030 idan suka kai ga samun karin jari, wutar lantarki, fasahohin zamani da kuma filayen noma, in ji bankin duniya a ranar Litinin.
A halin yanzu dai tsare-tsaren abinci ana kiyasta su zuwa dalar Amurka biliyan 313 a kowace shekara, kuma hakan zai karu zuwa uku idan gwamnatoci da masu kamfanoni sun sake yin tunanin karfafa manufofin siyasarsu da taimakonsu ga noma, zuwa ga manoma da masana'antun noma dake kwashe kashi 50 cikin 100 na ayyukan tattalin arzikin nahiyar.
"Lokaci ya yi na mai da noma da masana'antun noman Afrika, wani ginshikin kawo karshen talauci." in ji Makhtar Diop, mataimakin shugaban bankin duniya dake kula da shiyyar Afrika.
Kasashen Afrika na iyar kara yin amfani da kasuwannin shimkafa, masara, soja, suga, man kwakwa da sabbin makamashi, ta yadda za su iyar samun bunkasuwa tamkar manyan kasashen dake fitar da kayayyaki zuwa kasuwannin duniya a yankin Latin Amurka da shiyyar Asiya dake kudu maso yammanci suka samu, a cewar wannan banki mai hedkwata a birnin Washington na kasar Amurka. (Maman Ada)