Mai magana da yawun magatakardan MDD Martin Nesirky ya yi bayani ranar Talata cewa, babbar darektan hukumar abinci ta duniya (WFP) Ertharian Cousin za ta je kasar Burkina Faso yau Laraba don bayyana yanayin ci gaban bukatu na abinci da ake fuskanta a yankin na Sahel.
Ya ci gaba da cewa, wannan ziyara za ta yi ne shekara daya bayan hukumar tallafawa bil-adama har ma da hukumar abinci ta duniya suka kara yawan gudummawar, bisa bukatun abinci da kuma abincin gina jiki, da ake bukata cikin gaggawa a yankin Sahel.
Ya ce, a ziyararta ta kwanaki uku, madam Cousin za ta gana da wakilan gwamnatin kasar da sauran wakilai na cibiyoyin MDD da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
Burkina Faso bangare ne na yankin Sahel wadda ke fama da karancin abinci da matsalar tsaro da suka biyo bayan hambarar da gwamnatin Gaddafi a kasar Libya.(Lami)