Sin za ta yi wa hukumomin wurare daban-daban masu sa ido kan abinci da magunguna na kasar Sin kwaskwarima a cikin wannan shekara bisa shawarar da majalisar gudanarwa ta gabatar kan wannan lamarin.
Bisa wannan shawarar, gwamnatocin dake bisa matakai 3 wato na larduna, birane da gundumomi na kasar Sin za su koyi yadda majalisar gudanarwa ta daidaita hukumomi da kuma ayyukansu na sa ido kan abinci da magunguna. Tare kuma da kafa hukumominsu na wannan fanni bisa hakikannin halin da suke ciki, ta yadda za su gudanar da wannan aiki yadda ya kamata. (Amina)