Bisa labarin da aka samu, an ce, sunan wannan sabon shiri shi ne 'muryar masu fama da karancin abinci'. Bugu da kari a halin yanzu, hukumar ta FAO ta riga ta tsai da kudurin, na gwada wannan sabon shiri a kasashen Angola, da Habasha, da Malawi da kuma Nijar. Yayin da ake gudanar da aikin 'muryar masu fama da karancin abinci', za a zabi wakilan jama'a dubu daya zuwa biyar daga kowace kasa cikin kasashen 4, domin su amsa tambayoyi takwas, da haka, za a tantance ko cikin watanni sha biyu da suka gabata, wadannan jama'a da kungiyar ta zaba sun taba gamu da matsalar karancin abinci, ko a'a, tare kuma da fayyace yanayin fama da matsalar da suke ciki. (Maryam)