Ministan noman kasar Cote d'Ivoire zai fara wani rangadi tun daga ranar Laraba mai zuwa na yakin wayar da kan jama'a da fadakarwa domin sake bunkasa aikin samun albarkatun noma a yankunan tsakiya, arewacin kasar da arewa maso gabas da rikicin siyasa ke ratsawa daga shekarar 2002, tare kuma da barkewar tawaye har zuwa shekarar 2010 a cikin rabin arewacin kasar Cote d'Ivoire.
Wannan shela tana cikin tsarin aiwatar da wani shirin tallafawa samun albarkatun noma da kasuwancinsu da aka kaddamar a ranar 15 ga watan Disamban shekarar 2012 a Bouake, ta hanyar mai da hankali ga noman gandari na shimkafa, masara da kayan lambu.
Ana ganin wannan aiki zai taimaka wajen sake bunkasa samun albarkatun noma, musammun ma a bangaren cimaka a cikin jihohi 12 na wannan yanki da abun ya shafa bisa burin taimakawa rage talauci a yankunan karkara, ta yadda za'a taimakawa cigaban tattalin arziki a wadannan yankuna da aka kebe. (Maman Ada)