in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta janye wasu ma'aikatanta dake birnin Damascus na kasar Sham
2013-03-26 15:11:45 cri

Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky ya fadi a ran 25 ga wata cewa, MDD za ta janye wasu ma'aikatanta daga Damascus babban birnin kasar Sham bisa la'akarin da batun tsaron lafiyarsu.

A gun taron manema labaru da aka saba yi a birnin New York hedkwatar MDD, Martin Nesirky ya ce, daga ran 24 zuwa 25 ga wata, an kai hari a wurare dake kusa da wani Otel, da ma'aikatan majalisar suke zaune, lamarin da ya lalata gine-gine da motoci da dama.

Sashen kula da harkokin tsaron MDD, ya yanke shawarar ne bayan ya kimanta halin da ake ciki a yanzu, don haka za a janye wasu ma'aikata daga Damascus din nan da dan lokaci. Za a kuma kai galibinsu birnin Beirut, hedkwatar kasar Lebanon, da ofishin musamman mai kula da rikicin kasar Sham dake birnin Alkahira hedkwatar kasar Masar.

Martin Nesirky ya kara da cewa, an dauki wannan mataki ne bisa dalilan tsaro, MDD za ta ci gaba da dukufa kan taimakawa bangarori daban-daban na kasar Sham, wajen fitar da wata hanya da ta dace domin warware rikicin kasar. Don haka MDD ta girke ma'aikatanta a kasar, wadanda za su ci gaba da gudanar da ayyukan tallafin jin kai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China