Mr. Cai Weici, mataimakin shugaban gamayyar kungiyar masana'antun samar da kayayyakin injuna ta kasar Sin ya bayyana a ran 22 ga wata, cewar ko da yake yanzu masana'antun samar da kayayyakin injuna na kasar Sin suna ta samun ci gaba kamar yadda ya kamata, amma wasu sabbin sauye-sauye sun bullo. Alal misali, yawan darajar kayayyakin injuna da suka fitar bai kai na kayayyakin injunan da aka shigo da su ba. Kana kuma saurin karuwar yawan motocin da aka samar, kuma aka sayar ya ragu sosai sakamakon sauyin manufofin da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar, da kuma raguwar bukatar da ake da ita a kasuwa.
Mr. Cai ya ce, dole ne masana'antun samar da kayayyakin injuna na kasar Sin su canja kayayyakin da suke samarwa cikin hanzari a kokarin fama da sabon kalubalen da suke fuskanta. (Sanusi Chen)