Ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a watanni 3 na farkon wannan shekara, yawan karin darajar kayayyakin da masana'antun kasar Sin suka samu ya karu da kashi 11.6 cikin dari. Yawan sabbin mutane da suka fara amfani da wayar salula ya kai miliyan 32 da dubu 570, kana yawan wadanda suka fara amfani da internet ya kai miliyan 7 da dubu 550, sana'ar sadarwa ta bunkasa yadda ya kamata.
Babban injiniyan ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Zhu Hongren ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, ko da yake saurin bunkasuwar masana'antu ya ragu a watanni 3 na farkon shekarar bana, amma harkokin masana'antu na tafiya cikin kwanciyar hankali.
Ban da haka kuma, Mr. Zhu ya kara da cewa, ana fuskantar kalubale da dama daga gida da waje, bai kamata a kasa kula da raguwar yawan bukatun kasashen waje da kuma wahalhalun da kamfannoni suke fama da su ba.(Lami)