A wannan rana a gun wani taron kula da aikin tsimin makamashi da amfani da albarkatun masana'antu na birnin Nanjing, mataimakin ministan kula da harkokin masana'antu da sadarwa na kasar Sin Su Bo ya bayyana cewa, a shekarar bana, yawan albarkatun da masana'antu suke amfani da su a kasar Sin ya ragu da kashi 4 cikin kashi dari bisa na shekarar 2010, kana yawan iska mai dumama yanayi da ake fitar ya ragu da kashi fiye da 4 cikin kashi dari bisa na shekarar 2010.
Kana Su ya bayyana cewa, yawan ruwan da masana'antu suke amfani da su a bana ya ragu da kashi 7 cikin kashi dari bisa na shekarar bara.(Zainab)