Ranar Alhamis 19 ga wata, hukumar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta baiyanar da shirin bunkasuwar matsakaitan masana'antun kasar da su kara yawan kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasashen waje.Tsarin da ya soma daga shekarar 2011 da ta gabata zuwa 2015. Sin za ta kokarin sa kaimi ga wasu kamfanoni masu samar da injunan more rayuwa da su yi hadin kai domin fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje.
Shirin ya ce, Sin na sa kaimi ga wadannan kamfanoni da su kafa rassansu a wurare mafi tasiri na kasashen waje .Za su kuma kafa cibiyoyinsu wajen kera da yin sufuri da kuma sayar da kayayyaki, da bude kantuna ta hanyoyi daban-daban. Bisa shirin da aka yi, ana zaton cewa, daga shekarar 2011 zuwa ta 2015, yawan kudin da za a samu daga matsakaitan masana'antun kasar zai karu da kashi 9 bisa 100 a kowace shekara, yawan kayayyakin da za a fitar a ko wace shekara zai karu da kashi 7.5 bisa 100. Yawan kudin da aka samu daga wandannan kamfanoni kuma ya kai kashi 36 cikin 100 bisa na dukkan masana'antun.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin shekarar 2010, kawancan manyan kamfanoni ya kai kimanin 300, yawan kudin da suke samar a ko wace shekara ya kai kudin Sin RMB biliyan 3600.(Amina)