in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan motoci a kasar Sin zai zarce miliyan 200 a shekarar 2020
2010-09-05 20:49:05 cri
A ranar 5 ga wata, Wang Fuchang, mataimakin darektan sashen kula da masana'antu a karkashin ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin, ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2020, yawan motocin da ake da su a kasar Sin zai zarce miliyan 200, hakan nan kuma, matsalar makamashi da muhalli zai kara ci wa kasar tuwo a kwarya. Sabo da haka, rage hayakin da motocin gargajiya ke fitarwa da kuma bunkasa motocin da ke aiki da sabbin makamashi za ta zama wani babban aiki ga masana'antun kera motoci na kasar Sin.

A gun taron dandalin masana'antun kera motoci na kasar Sin na shekarar 2010, Wang Fuchang ya yi jawabin cewa, bunkasa motocin da ke iya aiki da dan makamashi da sabbin makamashi yana da muhimmanci sosai, kuma kamata ya yi kasar Sin ta dogara da karfin kanta kuma ta mai da hankali a kan kirkire-kirkiren sabbin fasahohi, da kuma hada gwiwa da kasa da kasa.

Har wa yau kuma, a gun taron, Liu Zhiquan, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fasaha a karkashin ma'aikatar kula da kiyaye harkokin muhalli ta kasar Sin, ya yi nuni da cewa, yanzu haka, kimanin kashi daya daga cikin biyar na biranen kasar Sin na fama da matsalar gurbacewar iska, kuma hayaki mai guba da motoci suke fitarwa ya zama babban sanadin gurbacewar iska.

A gun taron kuma, Du Shaozhong, mataimakin shugaban hukumar kula da kiyaye muhalli ta birnin Beijing, ya ce, domin kyautata ingancin iskar birnin, za a inganta ma'auni kan hayakin da motocin ke iya fitarwa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China