in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan ribar da masana'antun kasar Sin suka samu a watanni 3 na farkon wannan shekara ya ragu da kashi 1.3 cikin dari
2012-04-27 16:48:49 cri

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar da rahoto a ran 27 ga wata cewa, a watanni 3 na farkon wannan shekara, yawan ribar da manyan masana'antun kasar Sin suka samu ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 1040, wanda ya ragu da kashi 1.3 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.

Wani jami'in hukumar kididdiga ta kasar Sin ya bayyana cewa, yawan ribar da masana'antun kasar Sin suka samu ya ragu a watanni 3 na farkon wannan shekara a sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, sabo da haka, ana fama da wahalhalu wajen sayar da kayyayaki, kuma farashin abubuwan kera kayayyaki ya karu.

Kididdiga ta nuna cewa, daga cikin manyan masana'antun kasar Sin, yawan masana'antun samar da wutar lantarki da na'urorin samar da iska mai dumi ya karu cikin sauri a watanni 3 na farkon wannan shekara, wanda yawan karuwar ya kai kashi 28.3 cikin dari. Amma yawan ribar da masana'antun narka bakin karfe suka samu ya fi raguwa, wanda ya kai kashi 83.5 cikin dari.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China