Zhu Hongren ya yi wannan jawabi ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda ya ce, yanzu ana fuskantar matsaloli wajen samun raguwar tattalin arziki, yawan karuwar cinikayyar waje ya ragu, kazalika sakamakon wasu dalilai yawan kudin da aka samu wajen sayar da kayayyaki ya yi kasa sosai. Bayan haka kuma, masana'antun kasar Sin na fuskantar matsaloli da dama, ciki har da karuwar farashin danyun kayayyaki, da yawan kudin da suke biyan ma'aikata, da kuma shan wuyar hada-hadar kudi.
Bugu da kari, Zhu Hongren ya nuna cewa, a watanni 3 na farkon wannan shekara, yawan karin darajar kayayyaki da masana'antun kasar Sin suka samu ya karu da kashi 11.6 cikin dari. (Bilkisu)