Saurin karuwar ribar manyan masana'antun Sin ya kai kashi 22.8 bisa dari a watan Nuwamba
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fidda wani rahoto, wanda ke nuna cewa, adadin ribar da kamfanoni da masana'antu mallakar gwamnati, da masu zaman kansu wadanda ke cin riba fiye da yuan miliyan 5 cikin ko wace shekara, a watan Nuwamba na bana, ribar da suka samu ta kai yuan biliyan 638.5, adadin da ya karu da kashi 22.8 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kuma saurin karuwarsa ya karu da kashi 2.3 bisa dari idan aka kwatanta da na watan Oktoba na shekarar bana.
Sakamakon karuwar tattalin arzikin kasar, ribar da wadannan kamfanoni suka cimma nata ci gaba da karuwa.
A watan Agusta, adadin ribar da kamfanonin suka cimma ya ragu da kashi 6.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, amma a watan Satumba, adadin ya sake karuwa da kashi 7.8 bisa dari, inda kuma izuwa watan Nuwamba, adadin ya karu zuwa kashi 22.8 bisa dari.
Sakamakon karuwar adadin ribar da kamfanonin suka cimma cikin watannin da suka gabata, ana iya cewa, ribar da kamfanonin suka cimma a bana ta karu. (Maryam)