Game da wannan ma'aunin tattalin arzikin kasar a wannan shekara, rahoton ya ce, wasu alkaluma sun samu karuwa ciki hadda yawan kudi da aka zuba, cinikayyar shige da fice, ma'aunin yawan sayayya (CPI) idan kwatanta da na shekarar bara, amma yawan kudin da aka kashe wajen sayen abubuwa ya ragu.
Rahoton ya nuna cewa, komawa bayan tattalin arziki da aka samu daga shekarar 2012 na da dalili da tsarin da aka bi na canja hanyar samu bunkasuwa bisa matakai-matakai.
Mataimakin shugaban sashi mai bincike tattalin arziki na cibiyar Li Xuesong ya nuna cewa, a takaice dai, Sin za ta samu karuwar tattalin arziki, da karuwar farashin kayayyaki yadda ya kamata. (Amina)