Yawan kudin da kasar Sin ta samu daga sarrafa dukiyar kasa ya zuwa yanzu ya kai RMB triliyon 47, kimanin dalar Amurka triliyon 7.46. A bisa wannan alkaluma ne ya sa aka dogara da burin da kasar za ta cimma na samun yawan GDP da zai kai kishi 7.5 cikin 100, kuma tattalin arzikin zai bunkasa a kan hakan. Wen Jiabao ya furta haka ne a gaban manema labarai a karshen taron shekara shekara na majalisar wakilan kasar wato NPC.
Wen ya ce, hakika dai, tattalin arzikin kasar Sin ba ya bunkasa cikin sauri sabili da matsalar bashi a kasashen Turai da kuma dinbin bukatun kasashen waje.
A cikin irin wannan yanayi, domin rage bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wannan na nufin cewa, kamata ya yi a aiwatar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin kasar, cewar firaministan. (Abdou Halilou).